Jam’iyyar ‘yan Kwaminis mai mulki a China, ta bayyana sabon tsarin shugabanninta wadanda zasu rika yanke hukunci a kasar, wacce karfin tattalin arzikinta shine na biyu a duniya..
Sai dai kuma sabanin yadda aka saba a bisa al’ada, a wannan karon ba wata alama dake nuna wanda zai gaji shugaban, hakan yasa masu fashin baki ke ganin wannan wata alama ce dake nuna cewa yanzu shugaban China Xi Jinping na da karfin yin abinda ya ga dama, ba tare da an ja da shi ba.
Zhang Ming, mai fashin baki kan harkokin siyasa, wanda a kwanan nan ne yayi ritaya daga jami’ar Renmin dake birnin Beijing, ya ce shugaba Xi ya sauya tsarin shugabancin kasar, inda ya rage kimar kwamitin gudanarwa na kasar, ya mayar da su ba komai ba.
Firimiya Li Keqiang da Xi Jinping su kadai ne suka rage kan mukamansu a kwamitin, yayin da sauran mambobin biyar suka yi murabus.