Jam'iyyar dake Mulki a Liberia Ta Kalubalanci Sakamakon Zaben Farko

Mataimakin Shugaban kasar Liberia, dan takarar jam'iyya mai mulki, Unity Party da Goerges Weah, shahararren dan wasan kwallo wanda ya doke mataimakin shugaban kasar a zaben zagayen farko

A zaben shugaban kasar Liberia, mataimakin shugaban kasa wanda shi ne dan takarar jam'iyyar dake mulki, shi ya zo na biyu a sakamakon da hukumar zabe ta bayyana lamarin da ya haddasa jam'iyyar kalubalantar sakamakon.

: Jam’iyya mai mulki a kasar Liberia ta kalubalanci sakamakon zagaye na farko na zaben Shugaban kasa da aka yi, wanda dan takaranta ya zo na biyu ciki.

Jam’iyyar ta Unity Party ta zargi Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf, wadda mamba ce ta jam’iyyar, da yin katsalandan kan sakamakon zaben na ranar 10 ga watan Oktoba, saboda ta gana da alkalan zaben, abinda bai kamata ta yi ba.

Tsohon shahararren dan kwallon kafar nan George Weah ne ya zo na daya a zaben na 10 ga watan Oktoba, inda ya lashe kashi 38.4 cikin dari na kuri’un. Da yake ba dan takaran da ya sami kashi 50 cikin 100 na kuri'un da ake bukata, tilas aka shirya gudanarda zagaye na biyu na zaben a tsakanin shi Weah da mataimakin shugaban kasar, Joseph Boakai, wanda ya samu kamar kashi 28 cikin 100 na kuri'u a zaben farkon.

Zaben na ran 7 ga watan Nuwamba, ka iya zama karon farko da za a samu sauyin gwamnati a dimokaradiyyance tun daga 1944.