Babbar Jam’iyyar adawa a Janhuriyar Nijar, CPR Inganci ta yi babban taronta wato “Congre,” a birnin Damagaram, inda ta zabi jigonta Kassim Mukhtar a matsayin dan takararta na Shugaban kasa na zaben 2016.
Bayan taron, Kassim Mukhtar ya zanta da manema labarai ya shaida masu cewa tun bayan taron Maradi ne aka yanke shawarar tsai da shi dan takara. Y ace abin da ya sa aka tsai da shi dan takara shi ne ganin irin rawar da ya taka a matsayin Magajin Gari.
Alhaji Mukhtar ya yi takaicin abin da ya kira yawan ba da cin hanci da ake ta yi a kasar a maimakon a yi aikin gina kasa ko kyautata ma jama’a da irin wadannan kudaden. Yan a mai kira da aka kyautata bangaren shari’a don a yi adalci, sannan a kuma inganta tsaron kasa. Y ace bangern noma ma na bukatar a inganta sannan a samar ayyukan yi musamman ga matasa.
Ga Tamar Abari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5