Ingantchi Zata Shiga Zabe, Kuma Zata Bada Mamaki - inji Alhaji Illo

Tsohon ministan sadarwa, kakakin gwamnatin Nijer kuma tsohon Magajin Garin Maradi Mallam Kassoum Moctar

Wadansu magoya bayan dan takarar shugaban kasa, Kassoum Mamane Moctar a karkashin jam’iyyar CPR Ingantchi, sun fadi cewa suna tare da shi saboda irin ayyukan da suka gani yayi a Maradi.

Alhaji Mahaman wanda kuma aka sani da Illo mai turare jigo a jami’yyar CPR Ingantchi, ya fadi cewa abin da ake bukata shine ayi wa talakawa aiki, kuma sanin jama’ar jihar Maradi ne babu Magajin Garin da yayi aiki a jihar kamar Mamane Kassoum Moctarr a cikin shekaru 50 da suka wuce.

A shekarar 2016 ne dai aka shirya za a yi zabubbuka a janhuriyar Niger. Tambayar itace ko jam’iyyar CPR Ingantchi zata shiga zabe a shekara mai zuwa, ganin cewa shugabanta Mamane Kassoum Moctar yana tsare yanzu haka?

A wata hira da yayi da wakilin muryar Amurka Mani Chaibou, shugaban jam'iyar CPR a Maradi ya fadi cewa ko shugaban na tsare ko baya tsare, in Allah Ya yarda jam’iyyar zata yi aiki fiye da yadda ake tsammani.

"A duk jam’iyyun da ke fadin kasar, babu wadda ta sami karbuwa kamar jam’iyyar CPR Ingantchi, ta kuma kai duk inda wata jam’iyya ta kai don a duk fadin kasar, jam’iyyar na da ofisoshi har ma a kasar Belgique (Belgium)", inji Alhaji Illo.

Duk da cewa wasu na ganin kamar Kassoum Moctar yayi hanzari wajen tsayawa takara, Alhaji Illo ya ce ba haka take ba don kuwa yayi rawar gani a cikin shekaru uku da yayi yana aiki a matsayin Magajin Gari, fiye da wasu da suka dade suna aiki, don ko jaririn Jihar Maradi aka tambaya, in dai yana magana zai ce ga aikin da Kassoum yayi a jihar.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyyar CPR Inganci zata bada mamaki a 2016 - 1'45"