Hakan ya baiwa Shugaban na Indiya karin karfin gwiwa kan mulkinsa har zuwa ragowar lokacinsa. Jihar da take da mafi yawan jama’a, inda jam’iyar ta BJP ta murkushe jam’iyyar da ke mulkin yankin Samajwadi Party. ita ce babbar kyauta ta zabe ga jihohi biyar da suka yi zaben jin ra’ayin a wannan makon.
Modi yace “ Ina mika godiya ga al’ummar Uttar Pradesh, wannan nasara mai dinbin tarihi ga BJP nasara ce ta samun ci gaba da kyakykyawar gwamnati”. Modi da kansa ya jagoranci yakin neman zabe a Uttar Pradesh, bayan alkawarinsa mai rikitarwa na haramta amfani da manyan takardun kudi.
Kudurin da da yawa suka ji tsoron zai ware masu zabe a jihohin da suke talakawa. Amma bayan bayyana goyon bayan shugaban na Indiya, Jam’iyyar BJP ta sami babbar nasarar da babu wata jam’iyya da ta samu irin ta cikin shekaru goma a jihohin da ake artabu akansu.
A cewar kwamitin zabe, tazarar ta haura yawan kujerun 'yan majalisu 320 a majalisar da ke da mazaunai guda 403.