Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jam’iyyar APC, ta cika alkawari da ta yiwa ‘yan Najeriya cikin shekaru biyu da kama mulkin kasar.
Babban sakataren jam’iyyar na kasa Mai Malah Buni, yace babban abunda kasa take bukata saboda a sami ci gaba shine tsaro, kuma bisa dukkan alamu an sami haka.
Buni, wanda ya furta haka a hira da Madina Dauda, yace kada mutane su manta, shi da kansa ya gani, an girka abinci aka gudu aka bari, uwa mai goyo, ta bar jariri ta gudu, hatta bautan Allah wannan, an kai wani lokaci da aka kasa yin ibada a Najeriya.
Babban sakataren yace saboda idan akwai rashin tsaro, babu wani ci gaba na kwarai da za’a gani.
Yace koke-koken da ake yi yanzu cewa ana fama da ‘yunwa, da fatara, da sauran wasu batutuwa, duk suna fitowa ne yanzu saboda an sami zaman lafiya.
Ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa kuma, Mai Malah yace, ai ko ba komi, an saka tsoro a zukatun jama’a, yanzu ba’a yin satar kamar yadda ake yi da.
Kuma hakkin hukunta wadanda aka kama ya rata ne a kan banagrn shari’a, akawai bukatar mutane su saurara, su baiwa bangaren shari’a damar ta gudanar da ayyukanta.
Da yake amsa tambayar abunda yasa gwamnati ta rufe kan iyaka, tun gabannin a wadata kasa da abinci, sakataren na jam’iyyar APC yace, ai gashi yanzu an yi noma, kuma har za’a iya fitarwa waje, saboda kasa ta kara samun kudin shiga.
Your browser doesn’t support HTML5