Jamiyyar Apc ce ta Lashe Zaben Gwamna a jihohin Lagos da Ogun

  • Ladan Ayawa

Jamiyyar Apc ce ta lashe zaben Gwamna a jihohin Lagos da Ogun

JAMIYYAR APC CE TA LASHE ZABEN GWAMNA A JIHOHIN LAGOS DA OGUN

Sakamakon zaben gwammna da na yan majilisar jihohi da aka gudanar a jihohin kudu maso yammacin Najeriya, ya tabbatar da samun nasarar jamiyyar APC akan abokiyar hamayyar ta PDP.

Rahotanni daga hukumomin zabe daban-daban kama daga jihar Lagos da Ogun suka fitar ya nuna cewa jamiyyar ta APC tayi wa zaben cin kwan makauniya.

A jihar Ogun dan takarar jamiyyar APC Ibikunle Amosun ya samu kuriu dubu dari ukku da shidda da dari tara da tamanin da takwas (306,988) yayin da abokin hamayyar sa na jamiyyar PDP ya samu kuriu dari biyu da daya da dari hudu da arbain (201,440), Chief Ibikunle Amosun ya samu nasara ne a kananan hukumomi 11, yayin da na jamiyyar PDP ya samu nasara a kananan hukumomi 9.

Anan jihar Lagos kuwa hukumar zaben jihar ta bayyana dan takarar jamiyyar APC Mr Akinwumi Anbode a matsayin wanda ya lashe zaben wanda aka gudanar a ranar asabar da kuriu fiye da kuriu dubu dari takwas da goma sha daya yayin da shi kuwa abokin karawar san a jamiyyar PDP Mr Jimi Agbaje ya samu kuriu dubu dari shidda da hamsin da tara, wadannan kuriun dai an same su ne a kanana hukumomi 20 dake cikin jihar ta Lagos.

To sai duk da wannan nasarar da jamiyyar ta APC ta samu jamaa sun koka akanrashin fitowar masu zabe abinda aka alakanta da rashin baiwa zaben na gwamna da na yan majilisun jihohi muhimmamcin da yakamata, to ko yaya jamaa ke gani game da wannan zabe?

‘’Sunana Yahaya Platan, muna mile 12 Lagos hakikanin gaskiya karancin mutane wasu anan karamar hukumar mu da muke ciki kosofe Local Government wuri ne wanda ya tara jamaa da yawa na jihohin Najeriya, a bangaren mu wasu mutanen sun tafi gida domin acan suke da kuriar na dan takaran sun a gwamnoni da sauran su ko ba haka bane’’

‘’Sunana Kabiru Muhammadu Kontagora kuma zabe alhamdulillahi yayi kyau, mutane tsoron da suke ji bai auku ba domin akwai zaman lafiya kwarai da gaske’’

Ko da yake an kammala zaben cikin nasara a yankuna da dama da aka gudanar da wannan zabe, rundunar yan sanda na birnin Lagos tac ta kame wasu mutane da ake zargi da tada hankalin masu zabe da kuma fashin akwatunan zabe koda yake rundunar bata fadi wuri ko adadin wadanda aka kama ba, tuni dai jamaa suka fito domin ci gaba da harkokin su na yau da kullun.

Ga rahoton Babangida Jibrin.

Your browser doesn’t support HTML5

JAMIYYAR APC CE TA LASHE ZABEN GWAMNA A JIHOHIN LAGOS DA OGUN