Wani mamban babbar jam’iyar Democratic Alliance dake adawa a Afrika ta Kudu, ya ce kalaman da shugaba Jacob Zuma ke yi, tamkar shure-shure mutuwa ne, domin ya san cewa jam’iyarsa ta ANC za ta sha kayi a zaben kananan hukumomin da za a yi a ranar Laraba mai zuwa.
A ranar Lahadi, Shugaba Zuma ya yi kira ga ‘yan kasar da su zabi jam’iyya mai mulki ta ANC, domin jam’iyyar ta ci gaba da samar masu ababan more rayuwa.
Ita dai jam’iyar ta ANC, ita ke da rinjaye a birane 278 da ke kasar, amma kuria’r jin ra’ayin mutane da aka gudanar, ta nuna cewa akwai yiwuwar jam’iyar ta ANC ta sha kayi a biranen Pretoria da Johannesburg da Port Elizabeth.
Tsohuwar jakadar Afria ta Kudu Sheila Camerer, kuma mamba a jam’iyyar ta Democratic Alliance, ta ce a wannan karo, ‘yan kasar da dama ba za su saurari kalaman Zuma ba, domin sun san cewa babu wani sauyi a rayuwarsu.
Ta kuma zargi shugaba Zuma da yin amfani da dabaru na yaudara domin mutane su zabi jam;iyar ta ANC.