Shugabanin jamiyyar ZANU-PF na shugaba Robert Mugabe yau sun sallami Mugaben a matsayin shugaban jamiyyar kana sun nada tsohon mataimakin shugaban kasar Emerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban jamiyyar, idan dai ba a manta ba a cikin satin data gabata ne Mugabe ya kori mataimakin nasa wato Emerson.
Haka kuma shugabannin jamiyyar sun kori matar Mugabe Grace a matsayin shugaban Mata na jamiyyar, harma daga cikin jamiyyar gaba daya.
Yanzu dai idan Mugabe bai sauka daga kan shugaban cinkasar ba domin kashin kansa ba to abu na biyu da ka iya biyo bayya shine majilisar dokoin kasar ta tsige shi.
Mai tsawatarwa na majilisar dokokin kasar Innocent Gonese shine ya shaida wa kanfanin dillacin labarai na Reuters haka.
Kuma yanzu haka shugabannin jamiyyar MDC-T, dana ZANU-PF suna tattaunawa domin hada kaia majilisar.
Gonese yace muddin shugaba Mugabe bai sauka ba daga yau zuwa ranar talata to ba makawa abinda zai biyo baya shine tsigewa.
Har a zuwa jiya dubban matasa ne suka cika titunan birnin Zimbabwe wato Harare,domin gudanar da zanga-zangar kiran Mugabe ya sauka.