Masu zanga zanga sun hallara a gaban ofishin APC da suke neman kada dambarwar siyasa da ta kunno kai a majalisun tarayya su tarwats jam'iyyar.
Bisa ga alamu ra'ayinsu bai zo daya ba. Akwai wadanda suke son a hukunta 'yan jam'iyyar da suka buture mata wasu uma na ganin a cigaba da tafiya, wato a yafe abun da ya faru a majalisun tarayya.
Wasu na cewa jam'iyya ce gaba da kowa kuma duk wanda ya karya umurninta to dole a hukuntashi. Wai jam'iyya nada hurumin hukuntashi.Wasu sun ce ba zasu yadda wasu kalilan su bata masu jam'iyya ba. Sun ce makata yayi su shiga dakin taro su rufe kofa domin su samu sulhu.
Taron ya samu jagorancin shugaba Buhari inda shugabannin majalisar dattawa Bukola Saraki da na wakilai Yakubu Dogara suka kasance har da wasu gwamnonin jam'iyyar.
A taron shugaba Buhari yace ya zama wajibi a nemi yin takara a inuwar jam'iyya haka kuma ya zama wajibi a bi umurnin jam'iyya wurin nada mukamai.Wato jam'iyya ce kan gaban kowa domin ta samu ta cika alkawuran da ta yiwa 'yan Najeriya. Wannan wani kokari ne da shugaban ya yi na dinke barakar da ta barke a jam'iyyar.
Yanzu dai jam'iyyar na son a nada Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban masu rinyaje a majalisar wakilai. Suna kuma son sauke mataimakin majalisar dattawa dan PDP su maye gurbinsa da dan APC. gwamnonin APC zasu zauna da 'yan majalisar don yada manufar.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5