Jam'iyun siyasa 23 a jihar Borno sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya

Gangamin siyasa.

Rundunar yan Sandan Nigeria a jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria ta rattaba hannu akan wata yarjejeniya da jam'iyun siyasa 23 a jihar na tabbatar da an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana

Rundunar 'yan sandan Nigeria a jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria ta rattaba hannu akan wata yarjejeniya da jam'iyun siyasa 23 a jihar na tabbatar da an gudanar da zabubbukan da za'a yi cikin kwanciyar hankali da lumana.

An kula yarjejeniyar ce a hedikwatar yan Sanda dake birnin Maiduguri, inda dukkan wakilan jam'iyu 23 suka rattaba hannu akan yarjejeniyar akan da cewa ba zasu tada hankulan jama'a ko janyo rigingimu ba.

Kwamishin yan sandan jihar Borno Mr Clement Aduda yace gwamnati a shirye take ta gudanar da zabe cikin adalci. Yace idan wani abu ya faru, jam'iyun da suka rattaba hannu akan yarjejeniyar, su za'a dorawa laifi. Haka kuma kwamishin yan sandan yace idan aka kama mutum yana sayar da katin zabensa, to hukuma zata ci sa tarar naira miliyan daya ko kuma daurin shekara guda a gidan yari.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyun siyasa 23 a jihar Borno su rattaba hannu akan wata yarjejeniya