Jam'iyar PDP tace tayi nasarar hana mulkin jam'iya daya

Taron zumunci na siyasa

Jam'iyar PDP ta masu hamaiya a Nigeria tace tayi nasarar hana mulkin jam'iyar daya

Da alamu Nigeria ta kaure da masu son takarar shugabancin Nigeria a 2019 idan Allah ya kaimu, musamman ma bayan hadewar babar jam’iyar masu hamaiya ta PDP.

Sakataren shirye shirye na jam’iyar PDP Abdul Ningi ya cacaki jam’iyar APC wadda take jan ragamar mulkin Nigeria da cewa yanzu dai jam’iyar PDP tayi nasarar hana mulkin jam’iya daya a Nigeria.

Yace musamman zagin da aka yi musu a baya day ace sun tuba, sunce sunyi wau laifuffuka. Haka kuma yace abinda aka gani gara jiya da yau. Yana son ‘yan Nigeria suga da wace wahala ake ciki, su kuma ga yanzu wace wahala ake ciki,

Shi kuma sakataren jam’iyar APC wadda take jan ragamar mulkin Nigeria, Mai Mala Buni yace jam’iyar su bata yi aiki da kudi domin lamuran zabe ba. Yace a zabe da aka yi a 2015, da kudi zata yi tasiri da shugaba Muhammadu Buhari bai ci zabe ba.

Yace idan aka duba abinda ya faru, bayan zaben irin badakalar da aka yi akan kudin sayen makamai. Dukkan wadannan kudi idan aka duba an rabawa jihohi, an rabawa yan jam’iyar PDP saboda su fito su sayi kuri’u domin su kayar da jam’iyar APC.

Mallam Mala yace wadannan kudade da aka raba babu tasirin da suka yi, shi yasa am’iyar APC ta ci zabe. A saboda haka yace daga 2015, babu maganar tasirin kudi a harkar zabe, domin al’umman Nigeria kan su yaw aye ta yadda suka san shugabanin da zasu zaba wadanda zasu yiwa al’umma aiki.

Your browser doesn’t support HTML5

Siyasar 2019 a Nigeria 2"45