A tattaunawar shi da Grace Alheri Abdu ta Sashen Hausa na Muryar Amurka, Ali Sabo jigo a jam'iyar MNSD Nassara ta kasar Nijer ya nisanta jam'iyar ta su ta adawa da rigingimun da suka faru a sassan kasar ta Nijer, inda matasa da dama suka kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati, da ofisoshin 'yan sanda, da kuma farma wadanda ba Musulmi ba, tare da kokkona musu wuraren ibada.
Wannan sabon al'amari da ya kunno kai ya biyo ne bayan ziyarar da shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou ya kai kasar Faransa, ya tsaya tare da shugabannin kasashen duniya da suka hallara a birnin Paris su na goyon bayan mujallar barkwancin Charlie Hebdo ta kasar Faransa wadda ta yi zanen batanci ga Annabi Muhammad (saw).
Grace Alheri Abdu ta tambayi Ali Sabo ko da gaske ne jam'iyar su ta MNSD Nassara ce ta tunzura matasa su kai hare-hare, kafin Ali Sabo ya amsa, sai da ya tabo batun kona gidan ministan harakokin wajen Nijer Mohammed Bazoum da wasu matasa masu zanga-zanga suka yi a garin su:
Your browser doesn’t support HTML5