Wani jam'in tsaron lafiyar jama'a na "Civil Defence Corps" ya harbe abokin aikinsa a lokacin da suke farautar wani mai laifi, a yankin Araromi dake jahar Ondo.
Rahotani na nuni da cewa jami'an na Civil Defence, ba suyi amfani da horas war da suka samu dangane da sarrafa bindiga ba kamar yadda aka koya masu idan sun je gudanar da aikin su.
Kakakin rudunar 'yan Sandan jahar ta Ondo,Mr. Femi Joseph, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce jami'an na gudanar da aikin su ne na tsaron lafiyar jama'a ne amma daga bisani aka samu 'yar kuskure wanda yayi sanadiyar harbin.
Shi kuwa kakakin hukumar tsaron lafiyar jama'a ta Civil Defence, na jahar Ondo, Mr. kayode Balogun, ya tabbatar da batun amma ya karyata cewar jami'in Civil Defence ne ya yi harbin yana mai cewa daya daga cikin wadanda ake farauta ne ya ya harbi jami'in.
Ya kara da cewa a yanzu haka daya daga cikin wadanda suke farauta yana hannu kuma yana taimakawa jami'an wajen ci gaba da binciken da suke yi.