Banda wadannan jami'o'i guda goma sha bakwai da Jami'ar Jigawa ke cikinsu tana kuma da kawance da jami'o'in wasu kasashe dake nahiyar Asiya.
Mataimakin shugaban Jami'ar Farfasa Abdullahu Yusuf Arbado yace an kebe gurabe na musamman a jami'ar domin dalibai daga makwaftan kasashe. Ya kara da cewa a shekarar karatu ta gaba ne jami'ar zata kafa fannin karatun noma.
Burin da jami'ar ta sa gaba shi ne koyas da kananan malamansu su samu digiri na biyu da ma na uku. Sun hada hannu da Birtaniya domin cimma wannan burin.
Gwamnatin jihar tace ta yiwa jami'ar kyakyawan tanadi domin habakata inji mataimakin gwamnan jihar Barrister Ibrahim Hassan Hadeija. A kasafin kudin wannan shekarar gwamnati ta warewa jami'ar kudi nera biliyan uku saboda kammala wasu ayyuka da gwamnatin ta taras an fara yinsu. Kazalika gwamnati na shirin yin tanadin da zai kai jami'ar koyas da karatun kilita.
Jami'ar zata samar ma jihar ma'aikata da masu iliimin fasaha da kimiya na zamani.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5