Jami'an White House Basu Yi Mamakin Nasarar Shugaban Rasha Ba A Zaben Kasar

Shugaban Rasha Vladimir Putin yayinda yake murnar sake lashe zaben shugaban kasa

Fadar White House ta shugaban Amurka Donald Trump ta ce bata yi mamakin nasarara da shugaban Rasha ya samu ba yayinda ya sake lashe zaben shugabancin kasar karo na hudu

“Yan sa’oi bayan da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya lashe zabe, jami’an fadar White House sunce, nasararsa bata bada mamaki ba, kuma basu da niyar shugaba Donald Trump zai kira Putin ya taya shi murnar lashe zabe.

Wani kakakin fadar White House, Hogan Gidley yace, Amurka zata yi aiki tare da Rasha inda akwai damar yin haka. Gidley yace, “Zamu karfafa dangantaka da Rasha, zamu kuma ja daga idan Rasha tayiwa muradunmu barazana, sai dai zamu kuma nemi hanyoyin yin aiki tare idan zamu sami biyan bukatunmu”.

Sakamakon zaben da aka fitar jiya litinin, ya nuna Putin ya lashe zabe wa’adin mulki na hudu da kashi saba’in da bakwai cikin dari na kuri’un. Masu sa ido kan harkokin zabe na kasa da kasa a Moscow, da suka hada da jakade Jan Peterson na cibiyar harkokin tsaro da hadin kai sun bayyana cewa, “babu hamayya ta zahiri a zaben”.