Jami'an tsaro a jamhuriyar Niger sun kama tsohon kakkakin Majalisa

Jami'an tsaron kasar sun kama tsohon kakakin Majalisar dokokin Niger Hama Amadou, 'yan mintoci kalilan da saukar sa a filin saukar jiragen saman Jori Hamani..

Tsohon kakakin Majalisar dokokin jamhuriyar Niger Hama Amdou ya kwana a gidan yarin birnin Yaman.

Jami'an tsaron kasar sun kama tsohon kakakin Majalisar dokokin Niger Hama Amadou, 'yan mintoci kalilan da saukar sa a filin saukar jiragen saman Jori Hamani. Hama Madou ya koma Niger ne bayan yayi gudun hijirar watani goma sha biyar a kasar Faransa a saboda samacin da aka bayar a kansa bisa zrgin safarar jarirai.

Wani na kusa da tsohon kakkakin yace su ko kusa basu damu ba, in dai za'a yi shari;ar gaskiya, domin su suna murnar cewa ya koma kasar.

An yi hargitsi a filin saukar jiragen saman harma jami'an tsaron sun fesa wa mutane barkonon tsohuwa, ciki harda wakilin sashen Hausa Sule Mumuni Barma, wanda ya bada rahoton cewa an hana su shiga filin jirgin.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin niger ta kama Hama Amadou 2'29'