Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kaddamar Da Shirin Korar Wasu Falasdinawa

Wata Bafalasdiniya ta na duba gidansu da aka rusa

Jami’an Sojojin sun baiwa mutanen umurnin su bar Amona, wanda babbar kotun Israila ta yanke hukunci a shekarar 2014 cewar an yi gine-gine a wurin da yake mallakin Faladinawa mai zaman kansa, sannan dole a ruguje shi.

Da yawa daga cikin mutanen sun yi kokarin bijirewa dokar ta hanyar kunna wuta da jifa da duwatsu ga 'yan sanda, da kuma toshe hanyoyin shiga wurin da manyan duwatsu.

Wannan umurni na zuwa ne yayin da Israila ta ba da izinin gina gidaje 3,000 na mazauna a wani sabon wuri a gabar yamma da kogin ordan.
a jiya Talata Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta ce Firai minista Benjamin Netanyahu da Minsitan Tsaro Avigor Liberman suka amince da yin wadannan sabbin gine-gine.