Jami'an Tsaron Afghanistan Sun Murkushe Garkuwar da 'Yanbindiga Suka Yi A Birnin Kabul

Jami'an tsaro suna kai 'yansandan da suka jikata asibiti

Jamiian tsaron kasar Afghanistan sun kashe duka ‘yan bindigan nan 3 domin kawo karshen garkuwan da suka yi a tsakiyar birnin Kabul wanda hakan yayi dalilin ji wa mutane 6 rauni, inji mai Magana da yawun ministan cikin gida Sadeeq Seddiqi.

Yace an samu damar tserar da mutane 42 ba tare da ko kwarzane ba daga wurin dake da mahada da sansanin nan na jin kai na kasa da kasa wanda ke Shar-e-Naw dake kusa da babban birnin kasar.

An bada sanarwan wa daga sansanin a yau talata cewa maharan sunyi niyyar kai hari ne a wani ginin gwamnati dake kusa da ofishin jin kai dake Kabul.

Sanarwan tace anyi wa ginin illa amma an tabbatar cewa an samu nasarar kwashe daukacin maaikatan ba tare da ko mutum guda yaji ciwo ba.

Maharan dai sun fara kai harin ne ta tada bomb cikin mota kana suka bi da harbi bindiga tun daga daren jiya littini, Seddiqi yace nan da nan sojojin Afghanistan na musammam suka abka wa maharan inda suka suka shiga bude musu wuta.

Mai Magana da yawun Ministan cikin gida na kasar Afghanistan din yace da safiyar yau littini kuma aka ciugaba da bata kashi tsakanin sojojin Afghanistan din da su maharani