Jami'an Tsaro Sun Yi Arangama Da Masu Zanga-Zanga a Sudan

  • Ibrahim Garba

Shugaban bangaren Kudancin Sudan Salva Kiir kenan a kofar jirgin sama.

Rahotanni daga kasar Sudan na cewa jami’an tsaron kasar Sudan sun yi amfani da kulake wajen dukan dubban masu zanga-zangar kin jinin Gwaamnati, sannan suka rika bi suna kakkamasu suna tsarewa.

Rahotanni daga kasar Sudan na cewa jami’an tsaron kasar Sudan sun yi amfani da kulake wajen dukan dubban masu zanga-zangar kin jinin Gwaamnati, sannan suka rika bi suna kakkamasu suna tsarewa.

Shaidun gani daido sun bada kiyasin ganin ‘yan sanda akalla dari biyar dauke da kulake suna bin masu zanga-zangar suna duka a dandalin Abu Janzeer dake birnin Khartoum.

Masuzana-zangar kin jinin Gwamnatin Sudan suna kira ne da shugaba Omar al-Bashir ya sauka daga mulki. Mafi yawan masu zanga-zangar mata ne, mai Magana da yawun wadandasuka shirya zanga-zangar na jam’iyyar hamayya ta Umma Party Mariam al-Mahdi tace ‘yan sandan Sudan sun kame akalla jami’an kungiyar guda uku suna tsaredasu.

Shi kuma jami’in dake Magana dayawun hadin gwiwar jam’iyyun hamayyar kasar Sudan baki daya Faruk Abu Issa cewa yayi al’ummar Sudan zasu ci gaba da shirya zanga-zanga ta neman chanji a kasar Sudan, chanji na salon Demokuradiyya kamar dai yadda aka yi a kasashen Misra da Tunisia.