Jami'an Tsaro A Bauchi Sun Kwato Jamila al-Mustapha

Jamila al-Mustapha sanye da rigarta ta makaranta da kuma jakar makarantarta, ranar alhamis 18 Nuwamba 2010 a ofishin Hukumar Tsaron kasa ta Najeriya, SSS, dake Bauchi a bayan da aka kwato ta daga hannun mutanen da ake zargin sun sace ta makonni biyu kafin

Jamia'n tsaro daga hukumar tsaron kasa ta SSS sun damke mutane 6 da wasu muggan makamai a lokacin da suka kwato yarinyar da aka sace.

Tsohon rajista-janar na Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi Masu Zaman Kansu a Najeriya, Barrister Ahmed al-Mustapha, ya bayyana farin cikinsu a bayan da jami'an tsaro suka kwato 'yarsa mai shekara 11 'yar makaranta da wasu 'yan bindiga suka sace suka yi garkuwa da ita na tsawon makonni biyu.

A ranar alhamis cikin dare ne jami'ai na Hukumar Tsaron Cikin Gida ta Najeriya, SSS, a Bauchi suka kai farmaki wani gida dake Wuntin Dada, a kusa da babban birnin Jihar, inda suka kwato wannan yarinya mai suna Jamila. Haka kuma sun samu wasu muggan makamai, kamar irin bindigar nan mai jigida (machine gun) da wasu bindigogin.

Wadanda aka kama sun hada da wasu mazaje hudu da mata guda biyu.

Barrister al-Mustapha, ya bayyana cewa mutanen da suka sace 'yar ta sa, sun yi ta buga waya tare da aikewa da sakonnin "text", amma duk da damuwar da yake ciki, ya bi shawarar da hukumomi suka ba shi, ya ki yarda yayi magana da barayin.

Ya godewa jama'a a ciki da wajen Jihar wadanda suka taya su addu'a har Allah Ya maida musu da 'yarsu gida lafiya.

An bayyana cewa Jamila al-Mustapha tana nan cikin koshin lafiyarta, im ban da tsoratar da ta yi.

Ana iya sauraren hirar Sashen Hausa da mahaifin nata a saman wannan labari daga hannun dama.