Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Sun Fara Rangadi a Kasar

'Yan Sandan Najeriya.

Rundunar ‘yan Sandan Najeriya ta fara rangadin ‘kasar domin ganawa da shugabannin al’umma akan matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a sassan ‘kasar.

Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya mai kula da jihohin Arewa maso tsakiyar Najeriyar DIG Shu’aibu Lawal Gambo, wanda ya je jihar Neja, ya ce sufeto Janar ne ya umarcesu da su fita su gaida mutanen da suke aiki tare a duk fadin kasar.

Cikin wannan rangadi dai DIG Gambo, ya ce zasu ziyarci duk masu ruwa da tsaki a fannin tsaro da suka hada daga kan gwamnoni har zuwa sarakunan gargajiya da kungiyoyin al’umma.

Matakin ‘yan Sandan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka ‘kara samun gawarwakin wasu mutane hudu a cikin ruwa bayan wasu mutanen 22 da aka yiwa kisan gilla a ‘kauyen Ifogi dake karamar hukumar Makwa.

Kwamishin labaran jihar Neja, Mista Jonathan Batsa, ya tabbatar da cewa mutane 26 ne suka rasa rayukansu, inda suka nemi taimakon ‘yan sanda Najeriya da su aiko da ‘yan sandan ruwa na musamman domin su taimaka.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Sun Fara Rangadi a Kasar - 3'00"