A wata sanarwa da ma'aikatar sufuri ta fitar jiya Litinin tace za'a yanke shawarar yin nazari akan bayanan daga naurorin.
Sanarwar ta ma'aikatar ta biyo bayan da kamfanin jirgin Metroject ya sanar cewa hari daga waje ne ya yi sanadiyar tarwatsewar jirgin. Tun farko ba'a amince inji ne ya samu matsala ba ko kuma kuskuren matukin ne..
Kawo yanzu kamfanin Metrojet bai bada wata kwakwarar shaida ba akan abubuwan da ya fada. Haka ma ita ma'aikatar sufurin kasar Rasha tace furucin kamfanin tamkar riga malam masallaci ne.
Jirgin kamfanin Metrojet din yana dauke da fasinjoji wadanda yawancinsu 'yan Rasha ne da suka je yawon bude ido a kasar Masar. Suna kan hanyarsu ta komawa St. Petersburg ne can Rasha kafin jirgin ya tarwatse da yammacin Asabar mintuna 20 da tashinsa daga filin saukar jiragen sama dake Sham el-Sheikh, garin da mutane daga kasashen duniya ke yawan zuwa yawon bude ido.
Jiya Litinin gwamnatin Rasha ta soma kwashe gawarwakin mutanenta tana kaisu St. Petersburg inda yawancinsu suka fito.
To saidai hukumomin Rasha da na Masr sun yi watsi da ikirarin 'yan kungiyar ISIS reshen Masar cewa su ne suka kakkabo jirgin wai saboda yaki da Rasha ke yi da kungiyar a Syria. Hukumomin sun ce basa zaton 'yan ta'adan nada abun da zasu iya kakkabo jirgin da ya wuce mita 9100 a sararin samaniya