Yau littini ne Jami’an MDD su ka kai ziyara Rakhine bayan mahukuntar su dage wannan ziyarar asatin data gabata, yayin da adadin musulmai nay an jinsin Rohingya dake tserewa fadar da akeyi a arewacin kasar da ya shafi mutane kusan rabin miliyan guda.
Jami’an da suka hada da mai kula da ayyukan hadin gwiwa na majilisar, Renata Lok Dessallien, da wakilin shirin samar da abinci , kuma mukaddashin ayyukan hadinkai Domenico Scalpeli da babban jami’in kula da ‘yan gudun hijira suna cikin jeri tawagar da suka kai wannan ziyara ta yau kamar yadda majilisar ta ruwaito.
Sai dai ba a bayyana irin abinda wadannan jami’an ukku suka gani ba a wannan wurin da suka kai ziyara, inda aka bayyana cewa an samu yawan kone wurare mallakan musulmai akauyukan na Rahingya, tare daaikata fyade, kissa, da kwasan kayan mutanen tare da dasa boma-bomai kamar yadda mahukuntar ta Myanmar suka ce.
Rikici dai ya barke ne aranar 25 gawatan Agusta bayan da wasu ‘yan taaddan Rohingya suka kai wa wasu jami’an tsaron kasar hari, abinda yasa jami’an daukar matakin fansa .
Sai dai yanzu mahukuntar kasar sunce tun dafga ranar 5 ga watan Satunba ba a samu wani tashin hankali ba, ammadaikumabai dakatar da kwararan dubban ‘yan jinssin na Rohingya zuwa kasar Bangaladesh ba.