Jami’an kiwon lafiya a Laberiya na haramar tafiya yajin aiki biyo bayan rashin jituwa da aka samu dasu dangane da kudaden da ake biyansu, lamarin da ka iya kawo mummunan tsaiko ga yaki da suke yi da cutar Ebola.
Dubban ma’aikatan kungiyar ayyukan kiwon lafiya ta kasa, ko Liberia’s National Health Workers Association a turance sunce baza su je aiki ba yau Litinin, sai in har an kara musu albashi saboda hadarin aikin da suke yi na jinyar jama’ar dake dauke da cutar Ebola.
Wadannan ma’akata sun nemi a yi musu karin albashi na dala $700 akan dala $200 ko $300 da ake biyansu kowani wata.
Kasar Laberiya itace kasar da tafi kowacce adadin mutanen da suka kamu kuma suka rasa rayukansu daga cutar Ebola, lamarin da ya raba mutane sama da 2,300 da rayukansu a kasar dake fama da talauci.