Jami'an Diflomasiyan Amurka Sun Kira Rasha da Turkiya Su Kai Zuciya Nesa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry

Jami'an diflomasiyan Aurka da na sojojin sun kira Rasha da Turkiya su yi hattara kada takaddamar dake tsakaninsu ta rikide ta zama wani abu daban da zai fi na yaki da kungiyar ISIS

Jami'an difilomasiyyar Amurka dana sojinta suna kira ga Rasha da kuma Turkiyya su sassauta lafazinsu, suna masu nuna damuwa cewa ci gaba da gardamar da kasashen biyu suke yi kan harbe jirgin yakin Rasha cikin makon jiya kusa da kan iyakar Turkiyyar da Syria, zai iya kara zafafa lamari a yankin da tuni yake fama da tashin-tashina.

Jami'an tsaron Amurka sun fada jiya Litinin cewa Rasha ta karfafa matakan sojinta a Syria ta wajen girke makamaki masu linzami samfurin s-400 a sansaninta dake Sham din kamar yadda tayi alkawari. Haka nan jami'an na Amurka sun ce a karon farko Rasha ta yiwa jiragen yakinta samfurin Jet Su-34 damara da makamai masu linzami wadanda zasu iya kakkabo jirage a sararin samaniya.

Jami'an tsaron na Amurka sunyi gargadin cewa matakan daRasha take dauka abun damuwa ne wadanda zasu bude wani babi mai hadari na daukar matakai da ba zasu haifar da da mai-ido ba.Kuma su kawar da hankali daga yaki da kungiyar ISIS.

A wani yunkurin neman shawo kan lamarin, babban hafsan hafsoshin Amurka Janar Joseph Dunford, ya kira takwaran aikinsa na Rasha Janar Valery Gerasimov, wanda jami'ai suka bayyana cewa tattaunawarsu tana da ma'ana. Sai dai sunki su bada karin bayani kan abunda suka tattauna.