Jami’an tsaron dai sunce sun kame wannan mutumin ne a unguwar Meri dake cikin garin Maiduguri, bayan da suka gano yana sayar da wannan fom din ne Naira dari Uku ga kowanne dan gudun hijira, haka kuma ba a san tushen inda fom din ya fitoba.
Fom din na dauke da sunan Nigerian Network For Youth Science And Technology, wanda yanzu haka ke yawo a sansanin yan gudun hijira da sunan za a tallafawa mutanen da suka jikkata, sai dai wannan hukuma tace ta gono fom din na jabu ne kuma anayi ne domin damfarar al’umma.
Kwamandan Civil Defense na jihar Borno Abdullahi Ibrahim, yace kamata mutane su ankara game da irin wannan fom dake yawo a wannan sansani. Kuma an shirya shi ne domin damfara. Yakuma ce yanzu haka mutumin ya fadi cewa sun sayar da wannan fom har Naira Dubu Tara, kimanin Naira Miliyan ashirin da bakwai kenan.
A cewar mutumin da aka kama shima wasu mutane ne suka bashi domin ya sayar. Ya kamata al’umma su dunga la’akari da irin wadannan mutane da ke zagayawa sansanin yan gudun hijira da sunan cewa zasu basu tallafi kokuma biyan wasu kudade don karbar tallafi, wanda hakan ke nuni da cewa irin wadannan mutane sun kara yawaita a jihar Borno, ganin yadda halin da mutane suka shiga na neman tallafin gaggawa.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5