Jami'yyar APC Ta Sha Da Kyar A zaben 'Yan Majalisar Jihar Adamawa

Electoral commission officials check voting material at a polling station set up in the Shagari Day Secondary School in Yola, in Nigeria's Adamawa State, Feb. 22, 2019, on the eve of general elections.

Jam’iyyar APC dake mulki ta sha da kyar a hannun babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben majalisar dattawa da na wakilai da aka yi a jihar Adamawa.

Jam’iyyar APC ita ke da kujeru uku na majalisar dattawa da kuma kujeru takwas a majalisar wakilai.

‘Yar majalisar dattawa tilo daga arewa, Sanata Binta Masi Garba, ta fadi kujerar ta yayinda wani matashi kuma dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Mr. Ishaku Elijah Cliff ya lashe da kuri'u dubu saba’in da tara da dari uku da talatin da bakwai.

Farfesa Mamman Baba Ardo na jami'ar kimiya da fasaha ta Mautech shi ne ya bayyana sakamakon zaben.

Ya zuwa yanzu, wasu ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar APC sun rasa kujerun su ga babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Adamawa bisa sakamakon da aka bada.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami'yyar APC Ta Sha Da Kyar A zaben 'Yan Majalisar Adamawa - 1'12