Wannan wani abu ne da ake ganin a matsayin yunkurin kashe kanta da kanta ne bayan dat a sauka daga wata motar haya da ake kira UBER.
Matar wanda ake kira Adetutu Adedokun ta fada tekun ne ta kan gadar da ta raba birnin Legas gida biyu da ake kira third mainland.
Direban taxi da matar ta shiga ya ce yaji ta tana kace-nace da saurayinta kafin ta umarce shi ya tsaya akan gadar, inda nan da nan kuma ta bude kofa, kafin kace kwabo ta fada Ruwa.
Babban Daraktan hukumar bada agajin gaggawa a jihar Legas, Dr Olufemi Oke Osanyintolu, da kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce suna iya bakin kokarin su na gano matar da ran ta.
Gadar third mainland bridge dai tayi kaurin suna a yawan mutanen da ke kashe kansu da kansu a birnin Legas dama Najeriya baki daya, inda jama’a ke kira ga mahukunta su dauki matakan rigakafi akan gadar, domin hana mutanen da ke fadawa ruwa ta kan gadar da nufin kashe kansu.