Kwamandan tsaron rundunar Civil defense, Ibrahim Abdullahi ne ya gurfanar da wadannan mutane, ya kuma bayyana cewa hudu daga cikinsu an kama su ne da laifin satar wayoyin wutar lantarki da suka makare wasu motocin Pick Up guda biyu.
Sai kuma wanda aka kama a jami’ar Maiduguri, da na’urar kwamfuta, wanda aka ce ya kware ne wajan satar na’urori masu kwakwalwa da kuma wayoyin hannu na dalibai.
Da kuma wani dan kasar jamhuriyar Nijer, mai sana’ar yankan farce da aka kama da kudi sama da Dubu Dari Biyu a jikinsa amma rundunar ta ce zata mika shi ga hukumar shigi da fice domin gudanar da bincike a kansa tunda bashi da takardun shigowa Najeriya.
Matashin mai yiwa kungiyar boko haram leken asiri wanda ya ce su Uku ne kungiyr ta turo, ya bayyanawa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka cewa sunansa Ali Mustapha, daga kauyen Marte, kuma ya ce ya hallaka mutane dai dai har Goma sha uku.
Kwamandan jami’an tsaron Ibrahim Abdullahi, ya ce zasu ci gaba da gudanar da bincike da kuma mika dukkan masu laifin ga hukumomin da suka dace, ya kuma yi kira ga jama’a su rika sa idanu sosai akan irin wadannan bata gari.
Saurari rahoton Haruna Dauda Biu, domin cikakken bayani.
Your browser doesn’t support HTML5