Jami'an Tsaro Sun Kwace Gidan Buba Galadima

ABUJA: Buba Galadima da wasu 'yan APC dake neman ballewa

Jami’an tsaro sun mamaye gidan kakakin yakin neman shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, Buba Galadima a anguwar Wuse 2, da ke Abuja, babban birnin tarayya.

Ana zargin Buba Galadima da ake rashin biyan bashi da kudin ruwa daga shekarar 2004, wanda ya kai Naira miliyan 349.

Buba Galadima, wanda kafin lamarin ya ta’azzara, ya ce ya ga ‘yan sanda sun mamaye gidan sa amma bai san me su ke nufin aikatawa ba.

Daga bisani an fahimci cewa lamunin banki ne da Buba Galadima ya karba da nufin sayo takin zamani, amma a cewar sa, don hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI na binciken bankin shi yasa aka ki karbar takardar shaidar lamunin.

Ya zuwa locacin da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu el-Hikaya ya ke hada wannan labarin, jami’an tsaro sun umurci duk jama’ar da ke cikin gidan da su fice don za a karbi gidan a matsayin ajiya don biyan bashin kudin.

Buba Galadima ya ce sam ba zai fita daga gidan ba.

Za' a jira a ga yadda wannan lamari zai kaya don tuni wasu su ka fara alakanta shi da siyasa duk da cewa Injiniya Galadima bai ambata hakan ba.

A saurari cikakken bayani a rahoton Nasiru Adamu el-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

An Mamaye Gidan Buba Galadima a Abuja