Kasar Nijar ta shekara 25 da mulkin dimukuradiyya kamar yadda suka bukaci komawa wannan tafarki bayan kalubalantar mulkin soji.
WASHINGTON DC —
Mulkin siyasa abu ne da kasashen duniya ke shaukinsa ciki har da kasashenmu na Afirka. Jamuhuriyar Nijar ta cika shekaru 25 yanzu a tafarkin dimukuradiyya, to amma wasu suna ganin akwai sauran rina a kaba.
A baya suma Nijar sun yi fama da mulkin soji mna wajen shekaru 17 ba kakkautawa, wanda daga baya wasu dalibai suka botsare tare da fitowa kan tituna don nuna bukatarsu da mulkin siyasa.
Bayan kaiwa ga gacin fara mulkin siyasa, akwai kalubale iri-iri da kasar ke fuskanta haka zalika kuma akwai abubuwan ci gaban da ,ta samu a wannan tafarki.
Wakilinmu Sule Mumuni Barma ya tattauna da jama'a don jin ko kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa. a saurari sautin rahoton a makalar da ke kasa.
Your browser doesn’t support HTML5