Jamhuriyar Nijar-Martani Kan Sakamkon Zabe-Maradi

Zaben Nijar, wata mace kamin ta jefa kuri'arta.

'Yan hamayya a duk fadin jamhuriyar Nijar suna ci gaba da bayyana matsayarsu da ra'ayoyi kan sakamakon zaben kasar, wanda ya nuna tilas sai anje zagaye na biyu.

Da yake magana kan sakamakon zaben, shugabannin jam'iyyar Lumana Afirka a yankin Maradi, Malam Amadou Mamman Dutse, yace ikirarin cewa jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar cewa, a karon farko zata lashe zaben, Allah Ya sa kafa ya shure wannan ikirari, saboda haka babu abun godiya sai Allah.

Jam'iyyar ta Lumana tace ba zata sake wani salo ba, illa ta maida hankalinta wajen kara rokon Allah, da fatan Allada ya dafa mata a zagaye na biyu.

A ra'ayoyinsu da suka bayyanawa wakilin Sashen Hausa a yankin Maradi Chu'aibu Mani, da yawa sun yaba da sakamkon zaben, daga nan suka bayyana fatan Allah zabawa kasar duk abunda zai fi dacewa.

Zaben Nijar da aka yi ranar 21 ga watan nan, za'a yi zagaye na biyu ne, watau zaben fidda gwani ranar 21 ga watan Maris.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Martani kan zaben Nijar.