Wasu jam’iyun hamayya a Jamhuriyar Nijar sun kulla kawance karkashin jagorancin Dr. Adel Houbed na jam’iyyar MDR Tarna, domin abunda su ka ce, kare martabar tsarin mulkin demokuradiyya, wadda a ganinsu jam’iyyar PNDS Taraiya ta ke yi wa barazana.
Jam’iyun wadanda suka kira kansu ‘yan ba-ruwana’, sun ce tun bayan zaben kasar da aka yi a bara, jam’iyyar PNDS ta himmatu ne wajen yi wa dokokin kasar hawan kawara, ta wajen cin zarafin ‘yan hamayya da kuma ‘yan jarida.
Amma da yake maida martani wani kakakin jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar Abubakar Sabo, ya ce, ga ‘yan hamayya mulkin demokuradiyya yana nufin a kyale su su yi ta taka doka, amma idan aka yi musu magana, sai su ce ana take hakkinsu, ko ana keta tsarin mulkin kasa.
Wani dan hamayya Abdu Mamman kuma, ya ce babban abinda masu mulki suka maida hankali akai shine handama da cin hanci da rashawa.
Amma daya daga cikin masu magana da yawun gwamnati, ya ce ai ba’a taba yin gwamnati a Nijar wacce take yaki da cin hanci da rashawa kamar gwamnatin shugaba Muhammadu Issufou ba.
Hadakar jam’iyun ta jinjinawa jami’an tsaron kasar saboda jajircewar da suke ci gaba da yi, wajen yaki da mayakan sa-kai masu fakewa da addinin Islama.
Your browser doesn’t support HTML5