Kakaki sojojin dake yaki da kungiyar boko haram a yankin tafkin Chadi Kanar Mohammed Dole yayi wa wakilin sashen Hausa na VOA Hassan Maina Kaina Karin bayani.
Ga kuma abinda yake cewa.
‘’Za a turo kashi na farko a cikin yawan sojojin da Benintayi alkawari zasu turo nan Chadi.’’
Sai dai Hassan ya sake tambayar sa shin su dakaraun idan suka shigo cikin rundunar sojojin masu yaki da kungiyar ta boko haram a tafkin Chadi wani rawa zasu taka ne?
Nan ma ga abinda yake cewa
A cikin tsarin da akayi na kowane runduna kamar ta daya da take a Amora a cikin kasar Kamaru take ta biyu a cikinkasar Chadi take ta ukku a Baga Najeriya, ta hudu tana a Diffa Niger, su zasu zo ne domin tsaron Hedikwata ta rundunar gammayar kasashen dake fada da kungiyar ta boko haram kuma zata rika rakiyar maaikatan bada agaji wadanda zasu je ayyukan a wurare irin su wurin ‘yan gudun hijira, kana kuma it ace zata bada dauki na gaggawa na kowace runduna da take Najeriya, Kamaru da nan Chadi a duk lokacin da ake bukata.’’
Ga Hassan Maina Kaina da ci gaban rahoton 1’59
Your browser doesn’t support HTML5