Da yake magana a taron manema labaran, Dr. Khalid, yace kungiyar ta kira taron ne domin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na magana kan abun ashsha, da aika aika-aika game da kama jirgin shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya da wasu mutane a Afirka da kudade masu yawan gaske wai sun tafi sayo makamai.
Babban sakataren yace abun mamaki a gunsu shine da gwamnatin tarayya ta fito tace ai da saninta aka yi wannan shirin sayo makaman.
Dr. Khalid yace lallai lallai suna da yakini, cewa akwai hannun boye da yake shigan burtu a hare haren da ake kaiwa da sunan ta'addanci a Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5
Daga nan yaci gaba da yin tambayoyi wai shin ina mutanen da ake kamawa da zargin shiga ayyukan ta'adanci a wurare daban daban a Najeriya, ina aka kaisu, an yi musu hukunci kuma a ina?
Wakilin Sashen Hausa a Kaduna Isah Lawal Ikara ne ya halarci taron manema labaran kuma ya aiko bayanin.