Jama'ar Kano Sun Koka Akan Biyan Haraji

Yayin da gwamnatoci a matakai daban-daban a Najeriya ke kokarin fadada hanyoyin kudaden shiga biyo bayan faduwar farashin albarkatun mai a kasuwar duniya, galibin masu biyan kudaden haraji na bayyana rashin gamsuwa game da yadda hukumomi ke sarrafa kudaden da ake karba a wurin su.

Kamar yadda wani wanda bai fadi sunan sa ba ya ce "muna biyan haraji, daga karamar hukuma har zuwa gwamnatin jaha kuma yadda hukumar haraji tace mu biya haka muke biya kuma rasit-rasit din mu duk suna nan aje."

A cewar sa, muna biyan harajin ne a tunanin za'a yi mana aikace aikace kamar su gyaran hanya da sauran su, amma gaskiya ba wani abu har yanzu. malamin ya kara da cewa ko ruwan sa babu dan haka basu san abinda ake yi da kudin ba.

Jama'ar sun bayyana ra'ayoyin su da dama kuma yawanci sun ce suna biyan harajin ne amma ba tare da son zuciyar su ba, a cewar su, basu taba ganin amfanin biyan kudin ba.

Bincike ya nuna cewar bayan rashin kwarin gwiwar biyan kudin haraji ga hukumomi, akwai gazawar hukumomin wajan samar da sahihin tsarin biyan kudin harajin kamar yadda malam Abubakar Ahmad daya daga cikin masu kula da al'amura a Najeriya ya bayyana.