Jama'a da shugabanin kungiyoyi a jamhuriyar Niger sun fara maida martani ga bunkasar jama'a

Shugaban kasar Niger Mohammadou Isugu da shugaban Togo

A jamhuriyar Niger jama’a da shugabanin kungiyoyin addinin islama sun fara maida martani game da bunkasar da yawan al’umma a kasar

Masana yawan jama'a a jamhuriyar Niger sunyi hasashen cewa yawan al'ummar Niger zai ninka sau biyu zuwa miliyan 35 nan da shekaru 18 masu zuwa idan Allah ya kaimu.

Dalili ke nan yasa shugaban kasar Mahammdou Isuhu, ya ja halkulan jama'a gameda batun nunkasar yawan al'umma ba kakautawa.

Wakilin sashen Hausa Sule Mumini Barma ya aiko da rahoton cewa da alama wasu yan kasar basu gamsu da bayanan shugaba Isuhu ba.

Tuni jama'a da shugaanin kungiyoyin addinin suka fara maida martani, bayan da shugaban kasar Mahammadou Isuhu ya bayyana damuwa game da bunkasar yawan al’ummar kasar, inda masana suka gano yawan al'ummar kasar tana rubunyawa a duk shekaru 15.

A yayinda yake maida martani, wani mutum cewa yayi, wai shin su maganar da suke yi mata nawa ke gare su, ko kuma shin 'ya'ya nawa ke gare su.

Shi kumwa Mallam Alkasim Abdurraham yana ganin cewa daukan matakan bunkasa tattalin arziki itace hanyar tinkarar matsalolin jama'a.

Su kuma shugabanin addini sai suka shiga tunatar da jama'a akan abinda addini ya gargadi jama'a da shi akan batun kula da iyali.

Your browser doesn’t support HTML5

Martanin 'yan kasar Niger akan batun rage haihuwa 2"57