Jami'ar Amurka Ta Kayatar Da Dakin Kwanan Dalibai Da Na'urar Alexa

Wata jami’a a kasar Amurka ta kafa tarihi, wadda ta zama ta farko a fadin duniya da ta inganta dakunan kwanan dalibai, da na’urar ‘Alexa’ ita dai nau’rar ana yin amfani da ita wajen sauraron kade-kade ‘music’ kana da magana da wasu abokai a ko ina, haka kuma na’urar tana taya mutum hira da bashi labarai.

Na’urar zata taimaka wa dalibai wajen tunatar da su wasu abubuwa da suke da bukatar yi, da suka shafi karatun su ko wani aikin dake da muhimanci ga rayuwar su. Haka ma dalibai zasu iya amfani da na’urar wajen tambayar ta wasu bayanai, da suka shafi aikin da aka basu a azuzuwan su.

Jami’ar Saint Louis, ta sanar da cewar zata saka wannan na’urar a dakunan kowanne dalibi, ba tare da sun biya ko sisi ba, jami’ar za ta saka wannan na'urar kimanin 2,300. Dalibai kan iya amfani da na’urar wajen saye-saye a shafukan yanar gizo, kuma suna iya amfani da ita wajen bata umurni ta aiwatar da wasu ayyuka, kamar kunna wuta da kashewa, ko kunna AC da nau’urar dumama daki.

Na’urar zata taimakawa dalibai samun labarai da dumi-dumin su, da suka shafi abubuwan dake gudana a wasu makarantu da al’ummarsu.