Ga dukkan alamu za a fafata matuka a zaben gwamnonin jahohin Najeriya da ke tafe ranar Asabar, saboda kowacce daga cikin manyan jam’iyyun nan biyu, da ma wasu da ke biye da su, ta dukufa ba ji ba gani wajen ganin cewa ta kai labari.
Duk da rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da jam’iyyar PDP ta yi, wannan bai hana ta daura damarar gwabzawa a zaben gwamnonin jahohi ba. Hasali ma, jam’iyyar ta PDP ta cigaba da amfani da kalaman da ta yi amfani da su a yakin neman zaben shugaban kasa. Alal misali, Sakataren jam’iyyar ta PDP, Alhaji Umar tsauri, ya sake zargin cibayan tattalin arziki da wanzuwar kuncin rayuwa da tabarbarewar tsaro da rashin ayyukan yi da kuma shaye-shaye tsakanin matasa wai saboda takaici.
Su kuwa a nasu bangaren, ‘yan APC sun ce an yi kaca-kaca da Najeriya gabanin hawarsu mulki ta yadda sai da su ka yi da gaske kafin abubuwa su ka fara daidaita. Sakataren APC Mai Mala Boni ya ce don haka jam’iyyar APC ta himmantu ga kare nasarar da ta yi saboda kar PDP ta mayar da hannun agogo baya a matakin jahohi.
Sauran jam’iyyu ma irinsu PRP sun ce lalla za a dama da su a zaben gwamnonin. Dan takarar gwamnan jahar Bauchi karkashin PRP Furfesa Ali Pate ya yi zargin cewa ana wani abu shigin kama karya a siyasar kasar. Y ace da bukatar a yi koyi da salon siyasarsu.
Ga Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5