Jam'iyyar PDP Ta Lashe Adamawa

ADAMAWA: Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Jami’in ba da sakamakon zaben na jihar Adamawa, Farfesa Andrew Haruna shugaban jami’ar tarayya da ke Gashuwa, ya ba da sakamakon zaben inda dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Hon. Ahmadu Umaru Fintiri ya lashe zaben da 376,552.

Shi kuwa gwamnan jihar dan jam’iyyar APC Sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, ya sami kuri’u 336, 386.

Kuma jim kadan da bada sakamakon zaben sai magoya bayan jam’iyar PDP suka shiga murna a kusan daukacin jihar.

Kawo yanzu dai, gwamnan jihar Adamawan bai ce uffan ba tukunna, sai dai kuma wasu kusoshin jam’iyar APC a jihar sun bayyana cewa sun kadu da faduwar jam’iyar

Wannan nasara ta jam’iyar PDPn dai na zuwa ne yayin da a yau Jumma’a ake sa ran wani alkalin kotun jihar, Justice Abdul-Aziz Waziri, zai yanke hukunci a shari’ar da jam’iyyar MRDD ta shigar na kalubalantar hukumar zabe, INEC na cewa ba ta saka alama ko hoton jam’iyyar ba, watau logo a takardar kada kuri’a, na zaben gwamnan jihar da aka kammala.

Ita dai hukumar zaben na cewa, jam’iyyar ta MRDD, ba ta cika ka’idan tsayar da dan takara ba.

Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz domin jin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyyar PDP Ta Lashe Adamawa - 3'46"