Jam'iyyar APC maimulki a Najeriya ta dau alwashin ganin cewar babu wani dan adawa da zai rike wani mukami a mukaman Majalisar kasa. Dan takarar kujerar shugabancin Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume, ya bayyana manufar jam'iyyar ta su.
Inda yake cewa jam'iyya na kan matsayi na cewar babu yadda za a yi a raba mukamai dai-dai da dai-dai ko ace jam'iyyar adawa sun samu kaso maiyawa, don kuwa jam'iyyar APC ita ke da rinjaye a Majalisar.
Kuma yana ganin babu adalci ace jam'iyya ta fito ta nuna wanda take so a zaba don maye gurbin shugaban Majalisar Dattawa ko ta Wakilai, akwai bukatar a bar 'yan Majalisun su zabi abin da suke ganin shine yafi dacewa da kasa.
Ya bayyana cewar idan har Allah ya sa aka kammala zaben, kuma ya yi nasara yana kira da abokan takarar shi da su dauki kaddara, kamar yadda idan bai samuba zai dauki kaddara, haka kuma ya yi ma duk wanda aka zaba mubaya'a.
Ga kadan daga cikin hira da Sanata Ali Ndume.
Your browser doesn’t support HTML5