Jam'iyar PDP Ta Maida Martani Akan Dage Zabe

Yanzu haka dan takarar babbar jam’iyar adawa a Najeriya ta PDP, Atiku Abubakar ya maida martini game da dage babban zaben da aka shirya za’a gudanar a yau asabar.

Shugaban jam’iyar PDP a jihar Adamawa Barr. A.T Shehu, ya bayyana cewa akwai lauje cikin nadi a wannan lamarin ganin yanayin da aka dage baban zaben da aka shirya yi yau asabar.

Shima dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, yace nan bada jimawa ba, zasu gana da masu ruwa da tsaki don fitar da matsaya, kan dage zabe, amma shi ma ya nuna bacin ransa.

Tuni wasu ma’aikatan wucin gadi da aka dauka don gudanar da aikin zaben suka nuna bacin ransu, musamman wadanda aka tura yankuna masu nisa.

Ga karin bayani cin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyar PDP Ta Maida Martani Akan Dage Zabe-4'02"