Jam'iya Mai Mulki Ta Rasa Rinjaye A Majalisar Dattijan Najeriya

taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

Jam'iyar APC mai mulki ta koma marar rinjaye a majalisar dattijai biyo bayan sake sheka da sanatoci goma sha shida suka yi a dare daya, yayinda wadansu 'yan majalisar wakilai talatin da bakwai suka yi sallama da jam'iyar

Kallo ya koma Sama da Shaho ya dau Giwa. A Majalisar Dattawan Najeriya, jammiyar APC Mai mulki wadda a da ta ke da rinjaye, a yau ta koma marasa rinjaye, a zaman su na yau Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki ya karanta wata Wasika mai dauke da sunayen wadanda suka fice daga Jamiyyar.

Saraki ya ce mutane 14 sun koma Jamiyyar PDP, guda daya kuma ya koma Jamiyyar ADC.

A lokacinda ya ke yi wa manema labarai Jawabi, Sanata Abdulazeez Murtala Nyako wanda shi ne ya koma ADC, ya ce rashin adalci ne ya sa shi ya fita daga Jamiyyar APC, Sanata Nyako ya ce a Zaben Shugabani da Jamiyyar ta yi kwanaki, ba a yi wa shi da mutanen mazabar sa adalci ba saboda an hana su mukamai, kuma sun Kai kuka ga uwar Jamiyyar amma ba a saurare su ba.

A Nashi Jawabin Sakataren Jamiyyar APC Mallam Mala Buni ya ce abinda ya faru bai yi masu dadi ba amma haka demokradiya ta gada. Ya ce Kowa yana da yancin yin abinda ya ke so, Maimala Buni ya ce kofar su a bude ta ke na sulhu, kuma ana ta sulhu, saboda haka yana sa ran ya'yan Jamiyyar za su dawo a tafi tare. Sakataren ya Kara da cewa Jamiyyar ta cika da mutane masu mutunci, dole ne a samu matsaloli Amma ba za su hana Jamiyyar cigaba ba.

A saurari rahoton Medina Dauda domin Karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Majalisar Dattijai 15 sun fice daga APC-4"

Jerin Sunayen Sanatocin da suka fice daga Jam'iyar APC mai mulki:

1. Rabi’u Kwankwaso (Kano-Central)
2. Dino Melaye (Kogi-West)
3. Adesoji Akanbi (Oyo-South)
4.Monsurat Sunmonu (Oyo-Central)
5.Rafiu Ibrahim (Kwara-South)
6.Suleiman Hunkuyi (Kaduna-North)
7. Lanre Tejuoso (Ogun-Central)
8. Usman Nafada (Gombe)
9. Ibrahim Dambaba (Sokoto)
10.Mohammed Shittu (Jigawa)
11.Isa Misau (Bauchi)
12.Suleiman Nazif (Bauchi)
13.Shaaba Lafiagi (Kwara)
14. Barnabas Gemade (Benue).
15. Senator Abdul-Azeez Murtala-Nyako (Adamawa)