Jakadar kasar Sudan a Uganda, Najwa Abbas Gadaeldam ta rasu bayan da ta yi fama da cutar COVID-19 a birnin Khartoum.
Ana yi wa maragayiyar kallon wacce ta taimakawa fannin harkokin wajen kasar ta Sudan inda ta dabbaka harkokin wajen kasar da sauran kasashen duniya.
Najwa wacce ta rasu a ranar Laraba, ta rike mukamin jakadar Sudan a Uganda tun daga zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Omar Al Bashir, wanda shugabannin sojin kasar suka kifar da gwamnatinsa a watan Afrilun bara.
Hakan ya biyo bayan wata zanga zangar gama-gari da ta barke a kasar sanadiyyar hauhawar farashin bredi.
A kuma lokacin tana raye, marigayiya Najwa ta taba zama mai bai wa shugaban Uganda Yuweri Museveni shawara ta musamman kan harkokin da suka shafi Sudan da Sudan ta Kudu