Jajircewa Da Mayar Da Hankali Na Magance Kalubalen Neman Ilimi - Sumayya Bashir

Sumayya Bashir

Kamar kowacce matashiya bayan kammala sakandire gurbin karatun da Sumayya Bashir ta nema ba shi ta samu ba a duba da rashin samun makin da ake nema a jarabbawar share fagen shinga jami’a ba.

Matashiyar ta bayyana cewa ta so ta karanta harkokin kimiyyar sinadarai amma hakar ta bata cimma ruwa ba domin ta samu maki 39 ne a maimakon maki 40 da ake nema, sakamakon haka ne aka bata wani kwas daban.

Summaya, ta ce da ta fara karatun Library science, amma ta fuskanci kalubale domin kuwa lokacin da ta ke makarantar sakandare ajin daukar karatun kimiyya ta ke, dalili Kenan da ya sa fahimtar abinda ake koya mata ya zo mata daban da abinda ta saba.

Daga karshe ta bayyana cewa da jajircewa da mayar da hankali har ta fara gano yadda karatun yake, ko da shike ta fara ne da karatun diploma a wannan kwas kafin daga bisani ta sami gurbin digiri.

Bayan kammala karatun digiri Summaya ta ce bata sami aiki ba bayan yi wa kasa hidima amma ta sami damar cigaba da karatunta na digiri na biyu kuma tana taba harkar kasuwanci kafin ta samu aikin gwamntai ko na kamfani a cewarta.

Your browser doesn’t support HTML5

Jajircewa Da Mayar Da Hankali Na Magance Kalubalen Daukar Karatu - Sumayya Bashir 4 "56"