Jagoran 'Yan Awaren Kasar Spain Ya Mika Kai

  • Ladan Ayawa

Caele Puigdement, jagoran 'yan awaren Spain

Shugaban 'yan awaren kasar Spain ya mika kai shida wasu mutum hudu da suka gudu zuwa kasar Belgium, kuma suncea shirye suke su bada hadin kai.

Shugaban ‘yan awaren Caltalonia Carles Puidemont na kasar Spain, shida wasu ministoci hudu sun mika kansu a yau lahadi ga hukumomin birnin Brussels, biyo bayan bada umurnin kama su da gwamnatin Spain tayi.

Puigdemont ya fada cewa shi dama a shirye yake ya baiwa jami’an na birnin Brussel hadin kai sailin da ya isa wannan birni cikin satin data gabata.Ya fadi haka ne a shafin san a Twetter,Yace a shirye muke mu bada cikakken hadin kai gag a hukumar sharia na kasar Belgium biyo bayan umurnin kame su da kasarta Spain ta bayar ayi.

Babban mai shara’a na kasar ita ce ta bada umurnin kame Puigdemont kwana daya bayan ta tsare wasu mutane 9 dake da nasaba da wannan yunkurin warewar kafa sabuwar gwamnati, ta dai tsare su ne har sai an gurfanad dasu gaban kotu domin bayyana musu laifin sun a cin amanar kasa, sai kuma an bada belin daya daga cikin su.

Hari la yau babban kotun kasar ta Spain ta mika bukatar ta ga hukumomin ‘yan sandan kasa da kasa a kame puindgemont shida wasumukarabbansa hudu koda suka tsere daga Belgium din.

Babban mai gabatar dakara na kasar Belgium yace sun samu wannan takardan iznin kame ‘yan awaren kuma zasu fara yiwa Puingdemont tambayoyi nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa.