A cigaba da gasar cin kofin Nahiyar Afirka da akeyi na 'yan kasa da shekaru sha bakwai da haihuwa (Under 17) na 2019, wanda kasar Tanzaniya take dauke da nauyi gasar, inda kasashe takwas daga Afrika suke kece raini.
Kasar Kamaru ta tashi canjaros 0-0 tsakanisu da Senegal, sai kuma kasar Guinea ta samu nasara akan Morocco, da kwallo daya mai ban haushi a matakin wasan rukuni a ranar Lahadi da ta gabata.
Bayan kammala wasannin rukuni a ranar Lahadi, kasashe guda hudu sun samu kaiwa zuwa zagayen daf da karshe wato (Semifinal) a turance, kasashen sun hada da kasar Kamaru, Najeriya, Angola, da kuma Guinea.
A ranar Laraba 24 ga watan Afirilu 2019, za'a fafata tsakanin Kamaru da Angola, sai kuma Najeriya ta kara da kasar Guinea a matakin wasan daf da karshe.
Sakamakon nasarar da kasashen hudu suka samu na kaiwa matakin wasan daf da karshe a gasar ta 'yan kasa da shekaru 17, na Afirka yanzu haka su zasu wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya da za'ayi na 'yan kasa da shekaru sha bakwai a kasar Brazil shekara ta 2019.