Jadawalin Gasar Zakarun Kasashen Turai A Yau

A cigaba da fafatawa da ake yi cikin gasar cin kofin Zakarun Turai na bana a yau Talata 30 ga watan Afirilu 2019, za'a kara tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham wadda zata karbi bakoncin Ajax a matakin wasan daf da na karshe karawar farko.

Wannan ne karo na uku da kungiyoyin biyu za su fafata a tsakanisu cikin gasar zakarun Turai.

A karawar da sukayi Tottenham ta doke Ajax sau biyu, na farko ranar 16 ga watan Satumbar 1981 a gasar Euro Cup winners taci 3-1, sannan ta samu nasarar kwallaye 3-0 a Ingila a wasa na biyu ranar 29 ga watan Satumbar shekara 1981 kimanin shekaru 38 da suka wuce.

Ajax ta kawo wannan matakin sakamakon doke Real Madrid, da kuma Juventus, ita kuwa Tottenham ta fitar da Borussia Dortmund da kuma Manchester City.

kocin Tottenham Mouricio Pochetino ya zargi hukumar kwallon kafar Ingila da rashin adalci na
kasa ba su hutun da ya dace domin shirin tunkarar wasan su Ajax.

Amman ita Ajax hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Netherlands ta bata hutu a wasan lig domin shirya wa gasar.

Tottenham tana da 'yan wasa hudu da suka taka leda a Ajax, irin su Christian
Eriksen da Jan Vertonghen da Davinson Sanchez sai kuma Toby Alderweireld.

Ajax ta taba lashe gasar cin kofin zakarun Turai na Champions League,
a tarihin ta sau hudu ita kuwa Tottenham bata taba dauka ba.

Wasan dai za'a buga shine da misalin karfe takwas na yamma agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Ghana.