Jadawalin Gasar Cin Kofin Zakaru Na Kasashen Turai UEFA

A na cigaba da fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai (Uefa Champion League) na shekarar 2018/2019 a matakin wasa zagaye na biyu. Kungiyoyin kwallon kafa guda hudu ne a yau Laraba 13/3/2019 zasu barje gumi.

Barcelona ce zata karbi bakoncin Olympicos Lyon, a karawar su ta biyu inda a haduwarsu ta farko kungiyoyin sun tashi canjaras babu ci 0-0.

Haka ita kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus zata karbi bakoncin Liverpool na kasar Ingila a fafatawarsu ta farko an tashi 0-0.

Za'a buga dukkannin wasannin da misalin karfe Tara na dare agogon Najeriya, Nijar, Kamaru, da Kasar Chadi, duk kungiyar da ta samu nasara a cikinsu, zasu hade da kungiyoyi 6 da suka hada da Manchester United, Ajax, Manchester City, Tottenham, Fc Porto, da kuma Juventus, wadda suka samu hayewa zagayen gaba inda zasu kasance kungiyoyi takwas don fafatawa a wasan daf da na kusa da karshe na cin kofin zakarun Turai a bana.